Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da kara ta neman kare hakkokinsa na dan Adam tare da bukatar diyyar Naira Biliyan 1 a kan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaka da ita, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, tare da wasu jami’ai biyu, bisa abin da ya bayyana a matsayin mamaye gidansa da ke Abuja da bincike ba bisa ka’ida ba.
A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/345/2026 da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar 20 ga Fabrairu ta hannun lauyansa Oluwole Iyamu (SAN), El-Rufai na kalubalantar ingancin sammacin bincike da wani Babban Alkali na Kotun Majistare ta Babban Birnin Tarayya ya bayar a ranar 4 ga Fabrairu.
Yana rokon kotu ta ayyana sammacin da ya ba da izinin bincike da kwace kayayyaki a gidansa a matsayin mara inganci kuma wofantacce.
A cikin takardar karar, ya ce sammacin ba shi da inganci saboda rashin takamaiman bayani, kura-kuran rubutu masu muhimmanci, rashin fayyace yadda za a aiwatar da shi, yalwar iko fiye da kima, da kuma rashin hujjar zargi mai ma’ana, lamarin da ya ce ya saba wa Sashe na 37 na Kundin Tsarin Mulki.
Ya sanya Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaka da ita ICPC Aa matsayin wacce ake kara ta farko, sai Babban Alkali na Kotun Majistare ta Babban Birnin Tarayya a matsayin na biyu, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda a matsayin na uku, sannan Babban Lauyan Tarayya a matsayin na hudu.
El-Rufai na neman umarni guda bakwai, ciki har da ayyana cewa mamaye gidansa da ke Lamba 12, Mambilla Street, Aso Drive, Abuja, a ranar 19 ga Fabrairu da misalin karfe 2:00 na rana, wanda jami’an hukumar da rundunar ‘yan sandan Najeriya suka aiwatar bisa sammacin da ake takaddama a kansa, ya take hakkokinsa na asali.
Ya bukaci kotu ta ayyana cewa binciken ya zama babban take hakkin dan Adam, ciki har da tauye mutunci, tauye ‘yanci, rashin adalci a sauraron kara, da tauye sirri kamar yadda Sashe na 34, 35, 36 da 37 na Kundin Tsarin Mulki suka tanada.
Haka kuma ya roki kotu ta ayyana cewa duk wata hujja da aka samu ta hanyar sammacin da ba shi da inganci da binciken da bai dace ba, ba za a amince da ita a kowace shari’a a kansa ba, domin an samo ta ne ta hanyar karya kariyar kundin tsarin mulki.
Daga cikin sauran bukatunsa, yana neman a hana wadanda ake kara dogaro da duk wani abu da aka kwace daga gidansa a duk wata bincike ko tuhuma da ta shafe shi.
Ya kuma nemi a umarci hukumar da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda su gaggauta mayar masa da dukkan kayayyakin da aka kwace daga gidansa tare da cikakken jerinsu.
Bugu da kari, yana neman Naira Biliyan 1 a matsayin diyya ta gama-gari, ta misali da kuma ta tsanani kan take hakkokinsa, ciki har da kutsawa ba bisa ka’ida ba, kwace kayayyaki ba bisa doka ba, radadin zuciya, kunyatawa, tauye sirri da kuma bata masa suna.
Ya raba kudin da yake nema kamar haka: Naira Miliyan 300 a matsayin diyya kan radadin zuciya da damuwar rai; Naira Miliyan 400 a matsayin diyya ta misali domin hana maimaita irin wannan hali daga hukumomin tsaro; da Naira Miliyan 300 a matsayin diyya ta tsanani bisa abin da ya kira mugunta da danniya.
Haka kuma yana neman Naira Miliyan 100 a matsayin kudin shigar da kara da sauran kudaden shari’a.
A hujjojinsa, lauyansa ya ce sammacin binciken na da manyan kura-kurai, ciki har da rashin fayyace takamaiman abubuwan da za a kwace, kura-kuran rubutu, kalmomi marasa fayyacewa, da kuma rashin hujjar zargi tabbatacce.
Ya ce hakan ya saba wa Sashe na 143 zuwa 148 na Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka ta 2015, Sashe na 36 na Dokar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta 2000, da kuma kariyar kundin tsarin mulki da ke hana kutse ba bisa ka’ida ba.
A cikin takardar rantsuwar da aka gabatar don tallafa wa karar, Mohammed Shaba, Babban Sakatare ga tsohon gwamnan, ya ce jami’an hukumar da rundunar ‘yan sandan Najeriya sun mamaye gidan a ranar 19 ga Fabrairu bisa sammacin da ya ce na da matsala.
Ya ce sammacin bai fayyace kayayyakin da ake nema ba, kuma jami’an ba su bi ka’idojin doka ba kafin su gudanar da binciken.
Ya kara da cewa a yayin binciken an kwace wasu takardu da na’urorin lantarki na sirri, lamarin da ya jawo kunyatawa, radadin zuciya da damuwa.
Ya ce har yanzu ba a mayar da kayayyakin da aka kwace ba, kuma an shigar da karar ne domin tabbatar da kare hakkokin kundin tsarin mulki na wanda yake kara.













































