Taron shugabannin majalisar dokokin Najeriya ya bukaci a gaggauta gudanar da bincike kan gobarar da ta tashi a harabar majalisar dokokin jihar Kogi da ke Lokoja.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Abubakar Sulaiman, kakakin kungiyar ya sanyawa hannu kuma a ka rabawa manema labarai a Bauchi.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rawaito cewa a ranar 10 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai majalisar ta kone sakamakon wata gobara da ta tashi da tsakar dare.
Sulaiman wanda shi ne kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya jajanta wa kakakin majalisar dokokin Kogi Mista Matthew Kolawole kan tashin gobarar.
Shugaban ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su binciki lamarin don gano abin da ya jawo gobarar da nufin dakile sake faruwar ta.
Kolawole, wanda ya zanta da manema labarai, ya ce yana zargin zagon kasa ne tashin gobarar, amma bai bayyana inda ake zargin zagon kasan ba.
Anasa tsokacin kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa kwararrun kan tsaro da fasaha sun fara aikin gano musabbabin tashin gobarar da ta yi barna.












































