Shugaba Bola Tinubu da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 14 na wata ganawar sirri a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Sanusi dai ya dawo ne daga Jamhuriyar Nijar inda ya gana da gwamnatin mulkin soja da ta kwace mulki daga hannun zababben shugaban kasar Muhamad Bazoum.
Muhammadu Sanusi II ya isa fadar shugaban kasa ne da misalin karfe 8:25 na dare bayan wata babbar tawagar Malamai ta Najeriya ta gana da shugaban.
Da aka tambaye shi game da ziyararsa zuwa Nijar, sai tsohon Sarkin ya ce, komi lafiya, ba komai.
Izuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, Sanusi na ci gaba da ganawar sirrin da shugaban kasar.













































