Zamu Tabbatar Da Samarda Ruwan Sha Mai Tsafta Da Sauran Kayan More Rayuwa – Yusuf Datti.

0

href=”https://solacebasehausa.com/wp-content/uploads/2023/08/FB_IMG_1689933956449.jpg”>FB IMG 1689933956449

Aminu bala madobi.

Wakilin kananan hukumomin Kura, Madobi, Garun-mallam a Majalisar Wakilai Dr Yusuf Umar Datti ya jaddada kudirin sa na inganta rayuwar mutanen sa da ababen more rayuwa.

Datti, ya bayyana haka ne lokacin kaddamar da aikin samar da famfuna tuka tuka na zamani a garin Dan Marina duk a mazabar Gora dake karamar hukumar Madobi.

Dan majalisar wanda babban hadimin sa, Hon. Tukur Chinkoso ya wakilta, yace suna bin jadawalin ayyukan ne daya-bayan-daya domin tabbatar da ingancin aikin, yakuma jaddada cewa ba zasuyi kasa a gwiwa ba wajan cika dukkannin alkawuran dasuka dauka lokacin yakin neman zabe.

Tukur Chinkoso ya jaddada cewa, la’akari da irin halin da mutanen yankin ke ciki na rashin takamaiman gurin samun ruwa mai tsafta ya sanya daukan wannan matakan gaggawa don share musu hawaye.

Wakilin Dan majalisar wanda ke tareda Comrade Usama Burji sun tabbatar da cewa sun zo garin ne bisa amincewar Dan majalisar domin nazarin gurin da za a kaddamar da aikace aikacen.

Dan majalisar daganan ya tabbatar shirin sa na samar musu da kayan more rayuwa dasuka hadar da inganta kiwon lafiya, hanyoyi, wutar lantarki da makaranatun zamani dakuma uwa uba bayar da tallafi mai tsoka ga daruruwan matasan yankin.

Tun da farko dayake maida jawabi, guda cikin alummar yankin Dan marina, Salisu Usman ya godewa Dan majalisar bisa namijin kokari na cika alkawuran dayayi abaya.

Daganan Mutanen Dan Marinar sun bada tabbacin cigaba da bada dukkan goyon baya da hadin kan da ya kamata don samun gagarumar nasara a ayyukan gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here