Hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, ya ce ana killace shi tare da tilasta masa cin busasshiyar shinkafa.
Idan za ku iya tunawa a ranar 26 ga Yuli, 2023, sojoji suka tumbuke Bazoum tare da dakatar da tsarin mulkin kasar.
Shugaba Bola Tinubu, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), ya shirya wani taro bayan cikar wa’adin kwanaki 7 da kungiyar ta fitar na maido da Shugaba Mohamed Bazoum kan mukaminsa ya cika.
Gidan talabijin na CNN ya rawaito cewa Bazoum a cikin jerin sakonnin tes da ya aike wa wani abokinsa yana cewa “an hana shi hulda da mutane” tun daga ranar Juma’a, ba tare da wani ya kai masa abinci ko magunguna ba.
A cewar hambararren shugaban, ya shafe mako guda yana rayuwa babu wutar lantarki, al’amarin da ya zama ruwan dare ga daukacin ‘yan Nijar bayan da Najeriya ta katse wutar lantarki sakamakon juyin mulkin.
duk abincin da aka kawo masa ya lalace, kuma yanzu yana cin busasshen taliya ne da shinkafa.
Ko da yake an ki samun damar tattaunawa da mukaddashin sakatariyar harkokin wajen Amurka Victoria Nuland a ziyarar da ta kai Yamai babban birnin Nijar a ranar Litinin, Bazoum ta tattauna da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ta wayar tarho.













































