Hukumar ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Gaza ta ce Isra’ila ta hana ta shigar da kayan agaji a arewacin Gaza inda ake fama da ƙarancin abinci.
Shugaban hukumar Philippe Lazzarini, ya bayyana matakin da rashin tausayi.
Karin labari: Gwamnatin Tarayya ta fara shari’a da Binance kan kin biyan haraji
Mista Lazzirini, ya ce wannan yunƙurin na Isra’ila na nufin mutane da dama za su iya rasa ransu saboda yunwa da ƙishirwa da kuma rashin matsugunni.
Isra’ila dai ba ta mayar da martani a kan batun ba.