Kamfanin rarraba Wutar Lantarki na ƙasa TCN ya ce ya kammala dawo da layin wutar lantarki na Shiroro–Mando mai ƙarfin 330 kilovolt (KV) na biyu, bayan kammala aikin gyara.
Janar Manaja ta sashin Hulɗa da Jama’a na kamfanin Hajiya Ndidi Mbah ce ta sanar da hakan acikin wata sanarwa, inda ta bayyana cewa layin an kunna shi ne bayan injiniyoyin TCN sun kammala tsauraran ayyukan fasaha.
Mbah ta ce aikin gyaran an yi shi ne don tabbatar da inganci da amincin aikin kayan aikin, tare da bin ƙa’idojin tsaro da inganci sosai.
Ta kara da cewa dawo da dukkan layukan biyu na nuna babban ci gaba a ƙoƙarin TCN na ƙarfafa tsarin wutar lantarki da tabbatar da isar wutar lantarki mai dogaro ga dukkanin cibiyoyin su.
Mbah ta gode wa kwastomomi da masu ruwa da tsaki bisa haɗin kai da fahimta yayin lokacin da aka samu matsala, tare da tabbatar da ci gaba da gina tsarin wutar lantarki na ƙasa mai ɗorewa da inganci.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa TCN ta riga ta dawo da layin wutar lantarki na Shiroro–Mando na farko mai ƙarfin 330 KV.













































