Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba ta yanke wa mambobin kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya ke da hannu a harin 5 ga Yuni 2022, kan Cocin Katolika ta St. Francis Owo, a Jihar Ondo, inda suka kashe fiye da masu 40 tarr da raunata sama da 100.
Mai shari’a, Justice Emeka Nwite, ne ya yanke wannan hukuncin bayan ya samun Idris Abdulmalik Omeiza mai shekaru 25, Al Qasim Idris mai shekaru 20, Jamiu Abdulmalik mai shekaru 26 da Abdulhaleem Idris mai shekaru 25, da laifi kan tuhume-tuhume 9 na ta’addanci da Jami’an ‘Yansandan farin kaya (DSS) ta shigar a madadin Gwamnatin Tarayya.
Duk da haka, kotun ta wanke wanda ake kara na biyar, Momoh Otuho Abubakar mai shekaru47 bayan ta gano babu isassun shaidar da ke danganta shi da harin ta’addancin.
Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Nwite ya ce masu kara sun tabbatar da laifin wadanda aka yanke wa hukuncin ba tare da wani shakka ba, yayin da bayyana cewa shaidun da aka gabatar wa kotu sun nuna a fili cewa sun kasance mambobi ne, kuma masu hannu cikin ayyukan kungiyar ta’addanci da ke da alhakin kai mummunan harin cocin.
Kotun ta gano cewa wadanda aka yanke wa hukuncin manyan mambobi ne na kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab da ke aiki a Jihar Kogi kuma suna cikin wadanda suka kai hari kan cocin a lokacin ibadar Pentikost.
A cewar masu gabatar da kara, maharan sun kutsa cikin cocin inda suka yi garkuwa da masu ibada, sannan suka tashin hankalin da ya haifar da mummunan asar rai da lalata wurin.
An rawaito maharan sun yi amfani da abun fashewa da aka kirkira IED da bindigogin AK-47 wajen kai harin domin ciyar da akidarsu ta tsattsauran ra’ayin addinin gaba.
Don tabbatar da tuhumar, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu 11 kuma sun mika kayan 23 ciki har da furucin ikrarin laifi da rahoton binciken fasaha na dijital.
Daga cikin kayan da kotu ta amince da su akwai wata wayar technophone da ake zargin tana dauke da tattaunawa tsakanin wadanda ake kara kafin da bayan harin.
Daya daga cikin shaidun masu gabatar da kara, wanda tsira daga harin, ya yi bayanin da ke tsoratarwa kan yadda maharan suka tashi akalla na’urorin fashewa uku a cikin coci, wanda ya haifar da firgici da zubar da jini tsakanin masu ibada.
Mai shari’a Nwite ya ce dukan shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar sun danganta wadanda aka yanke wa hukuncin hudu da harin kuma an same su da laifin ta’addanci.












































