Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ziyarci tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, da limamin coci Fasto Tunde Bakare a Legas.
Mai baiwa El-Rufai shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ne ya bayyana ziyarar a cikin wani sakon Twitter a ranar Lahadi.
Ganawar El-Rufai da manyan mutane biyu na zuwa ne kwanaki kadan bayan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kaduna.
Karin karatu: Tinubu ne yaƙi amincewa da naɗi na a matsayin minista, ba majalisar dattawa ba – El-Rufai
Kasancewar sa a Legas ya haifar da sabon cece-ku-ce game da makomar siyasarsa da kuma dabarun kawancen da zai yi gabanin zaben 2027.
Aregbesola, wanda tsohon gwamnan jihar Osun ne a karo na biyu, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a kwanakin baya bayan da aka dade ana rikicin cikin gida a jam’iyyar reshen jihar Osun.
Shi kuwa Bakare na cikin shahararrun muryar siyasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.