Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce bai dace gwamnati ta ci gaba da tattaunawa da ‘yan ta’adda ba, inda ya bayyana cewa dole Najeriya ta ɗauki mataki mai ƙarfi tare da karɓar taimakon ƙasashen waje domin fuskantar matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara.
Obasanjo ya yi wannan magana ne a taron Bikin Kirsimeti da Yabo na Jihar Filato da aka gudanar a birnin Jos a ranar Juma’a, inda ya jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnatoci za su daina neman afuwa ko tattaunawa da masu aikata ta’addanci.
Ya yi wannan jawabin ne a daidai lokacin da ake fama da kashe-kashe, garkuwa da mutane da hare-hare a yankunan Arewa a makonnin baya-bayan nan.
A ranar 21 ga Nuwamba, an yi garkuwa da dalibai 315 da malamai 13 daga makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri a jihar Neja, lamarin da ya faru kwanaki bayan sace dalibai mata 26 a sakandiren yan mata da ke Maga a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi a ranar 17 ga watan Nuwamba.
A sabon harin da ‘yan bindiga suka kai ƙauyen Palaita a unguwar Erena, ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja, mutane 24 suka ƙunshi ciki har da mata masu juna biyu aka yi garkuwa da su a gonar shinkafa.
Haka kuma kusan mutane 20 aka sace a Kano da Kwara tsakanin daren Litinin da safiyar Talata, yayin da wasu 38 da aka sace daga majami’ar Christ Apostolic Church, Oke-Isegun, Eruku a jihar Kwara a ranar 18 ga Nuwamba aka sako su bayan gwamnatocin tarayya sun tattauna da wadanda suka sace su.
A harin Talata ma, mutane 10 da suka haɗa da mata masu juna biyu, iyaye masu shayarwa da kananan yara aka ƙwace a ƙauyen Isapa, kusa da Eruku a jihar Kwara.
Da yake jawabi a Jos, Obasanjo ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa, yana mai cewa ‘yan Najeriya na da haƙƙin neman taimakon ƙasashen waje idan gwamnati ta gaza kare su.
Ya ce ‘yan Najeriya na fuskantar kisa, yayin da gwamnati ta kasa samar da kariya, don haka ya dace a nemi taimakon ƙasashen da za su iya yin abin da gwamnati ta kasa yi.
Obasanjo ya kara da cewa a zamaninsa ba a da ingantattun hanyoyin gano maboyar ‘yan ta’adda kamar yadda ake da shi yanzu, wanda a yanzu fasahar zamani kamar drones na da ƙarfin kama masu aikata laifi a ko’ina.
Ya bayyana cewa gwamnatin ƙasar na da ƙarfi ta amfani da irin waɗannan kayan aiki, don haka ya tambaya me ya sa ake jingina komai ga neman afuwa ko tattaunawa da ‘yan ta’adda maimakon ɗaukar matakin da ya dace.













































