Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo ta kama wani mutum mai shekara 38 mai suna Nsikak Kingsley da ake zargin dukan mahaifinsa, Adone Peter, har lahira a garin Oda da ke Karamar Hukumar Akure ta Kudu a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ya fitar a ranar Alhamis.
A cewar Jimoh, wanda ake zargin ya aikata wannan mummunan aikin ne bayan wani sabani da ya barke tsakaninsa da marigayin, lamarin da ya rikide zuwa fada.
Sanarwar ta ce, “Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Felix Ohagwu, ta kama wani mutum mai shekara 38 mai suna Nsikak Kingsley kan zargin hannunsa a mutuwar mahaifinsa, Adone Peter, mai shekara 65.
“Binciken farko ya nuna cewa a ranar 28 ga Mayu, 2026, wanda ake zargin ya samu sabani mai zafi da mahaifinsa wadda ta rikide zuwa fada. A lokacin fadan, an ce marigayin ya ji mummunan rauni, musamman a ka. Nan take aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar gaggawa.
“Abin takaici, duk da kokarin likitoci, likitan da ke kula da shi ya tabbatar da mutuwarsa yayin da ake masa magani.”
Ya kara da cewa rundunar ta samu damar kama wanda ake zargin ne bayan dan’uwansa ya kai rahoton korafin a wani ofishin ’yan sanda da ke kusa, sannan jami’ai suka shiga aiki.
A shekarar 2024, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Lagos ta tsare wani matashi mai shekara 25, Chibunnma Chimelie, da ake zargi caka wa mahaifinsa mai shekara 68 wuka har ya mutu.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 10:00 na dare a yankin Isolo da ke jihar.












































