Da Dumi-Dumi: Kotu a Kano ta sake ba da sabon umarni kan dakatar da Ganduje daga APC

Ganduje, kotu, dakatar, umarnin, APC, shugaban, jam'iyya
Wata babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Usman Mallam Na'Abba wadda tun farko ta tabbatar da dakatarwar da aka yiwa Dakta Abdullahi Umar Ganduje...

Wata babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Usman Mallam Na’Abba wadda tun farko ta tabbatar da dakatarwar da aka yiwa Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin dan jam’iyyar APC, tare da hana shi bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa ya sauya sheka, inda ya fice daga jam’iyyar.

A ranar Litinin 22 ga watan Afrilun 2024, Mai Shari’a Usman Mallam Naaba, wanda ke jagorantar babbar kotun jihar Kano, ya bayar da umarnin dakatar da aiwatar da umarnin wucin gadi da ya bayar a ranar 17 ga watan Afrilu, 2024.

Karin labari: Shugaba Tinubu ya yi kira a samar da cibiyar yaki da ta’addanci a Afrika

Wannan umarnin ya umarci wadanda abin ya shafa da a ci gaba da kasancewa a yadda suke a ranar 15 ga watan Afrilu 2024 game da dakatarwar da ake zargin shugabannin mazabar Ganduje sun yiwa Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

SolaceBase ta rawaito cewa Haladu Gwanjo da Laminu Sani Barguma da suka yi ikirarin cewa suna cikin shugabancin jam’iyyar APC na mazabar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar, su ne suka karbo umarnin tabbatar da dakatar da Ganduje a kotu, bayan sun dakatar da shi daga jam’iyyar.

Karin labari: Gwamnatin jihar Kwara ta rufe kasuwar saida nama ta Mandate

Wadanda suka shigar karar sun hada da kwamitin amintattu na jam’iyyar APC ta kasa, da jam’iyyar APC a matakin jihar Kano da kuma Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Umarnin na wucin gadi ya soke aiwatar da umarnin wucin gadi da ke kunshe a cikin hukuncin da kotun ta yanke a ranar 17 ga Afrilu, 2024, inda ta umarci bangarorin da su kiyaye matsayinsu na bayan kamar yadda suke a ranar 15 ga Afrilu, 2024 dangane da batun.

Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Afrilun 2024 don sauraron karar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here