A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin jihar Kwara ta rufe mayankar da ke kasuwar Mandate da ke Ilorin na wani dan lokaci domin ba da damar yin hayaki da tsaftace yankin baki daya.
Ci gaban ya biyo bayan zargin gubar nama da aka rawaito a wurin.
Dokta Abubakar Ayinla, babban sakataren ma’aikatar muhalli, ya ce matakin wani bangare ne na kokarin kare jama’a daga lamarin.
Karin labari: Hukumar FRSC ta kama Direban kamfanin BUA da ya murkushe mutane 6 har lahira a hanyar Kano zuwa Zariya
A cewarsa, za’a sake bude mayankan a ranar Laraba.
“Wannan sabuntawa ne ga rahoton baya game da ci gaban da aka samu a kasuwar Mandate.
Jami’an gwamnatin jihar Kwara da kwararru sun isa kasuwar Mandate domin samar da matakan kare lafiyar jama’a sakamakon jita-jitar naman saniya mai guba.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: EFCC na neman tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo
“Nan da nan tawagar ta kwace dukkan naman da ake zargi don gwaje-gwaje da kuma tabbatar da fara hulda da masu ruwa da tsaki na Kasuwar Mandate.”