Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce wani dattijo mai shekaru 60 mai suna Malam Danjuma wanda aka fi sani da “Black” da dansa Ibrahim mai shekaru 35 da kuma wani Aminu Gaye mai shekaru 35 sun mutu.
Hakan ya faru ne a lokacin da suke kokarin dauko wayar salula daga bayan gida, a kauyen ‘Yar Gwanda da ke karamar hukumar Tsanyawa ta jihar.
Alhaji Saminu Abdullahi, mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Kano ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Karin labari: Gwamnatin jihar Kwara ta rufe kasuwar saida nama ta Mandate
Sai dai ya ce an ceto wani Abba Alasan mai shekaru 28 da ransa daga wurin.
Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi.
A cewarsa, “Mun samu kiran gaggawa daga tashar kashe gobara ta Tsanyawa da misalin karfe 11:00 na safe daga wani Aminu ‘yar gwanda, cewa wasu mutane 4 sun makale a cikin bayan gida.
Karin labari: Rundunar Yan Sanda Najeriya Ta Janyewa Yahya Bello Jami’an tsaron dake kula da shi
“Nan take mun aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:15 na safe.
“Danjuma yana kokarin dauko wayar salular da ta fada ramin bayan gidan ne a lokacin da ya makale. Bayan haka, dansa ya shiga bandakin ramin don ya ceci mahaifinsa shi ma ya kama shi.
“Gaye da Alasan suma sun shiga ne domin ceto mutanen biyu kuma sun makale,” in ji shi.
Karin labari: Mutane 23 sun rasa ran su a wani hari da yan ta’adda suka kai jihar Kaduna
Abdullahi ya ce an kubutar da mutum 3 na farko a sume yayin da aka ceto na hudun da ransu.
Ya ce an mika dukkan wadanda abin ya shafa ga Sufeto Iro Lado, a sashin ‘yan sanda na Tsanyawa.
Jami’in hulda da jama’a ya ce ‘yan sandan sun kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa Asibitin musamman na Bichi domin kula da lafiyarsu inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwar mutane ukun daya kuma da rai.