Daga Khadija Bello Waziri
Rundunar yan sandan Najeriya ta janyewa tsohon gwammnan jihar Kogi Yahaya Bello jami’an tsaron da suke kula da shi.
Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan da hukumar da ke yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta bayyana neman sa ruwa a jallo.
Tsohon gwamnan Kogin yaki halartar zaman babbar kotun tarayya dake Abuja, ana zargin sa, shubaman ma’aikatan jihar Kogi, Alli Bello da kuma Dauda Sulaiman da karkatar kudin jihar da suka kai kimanin naira billiyan 80.2
Bayan da rundunar yan sanda ta bada sanarwar janyewa Yahaya Bello jami’an tsaro, ita kuma hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) ta sa shi a cikin jerin mutanen da take nema.