
Wasu ‘yan bindiga su 8 sanye da bakaken kaya sun kai hari Ajadeh Event Centre da ke Iperu Remo daura da hanyar Sagamu, inda suka kashe wani malami a Jami’ar Babcock Ilisan Remo mai suna Yinka Olowojobi yayin da suka yi awon gaba da wasu guda biyu a yayin harin.
Sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ya fitar a ranar Litinin, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Afrilu da misalin karfe 9:20 na dare.
An ce ‘yan bindigar sun harbi Olowojobi a kirji bayan sun yi zargin sun ki tafiya tare da su.
Karin labari: Mutane 3 a Kano sun mutu harda wani Dattijo kan dauko wayar salula daga bayi
Malamin jami’ar Babcock da aka kashe tare da wani Dare da kuma wani mutum da har yanzu ba a tantance ba da aka sace an ce suna cikin shakatawa a dakin taron yayin da wadannan gungun ‘yan banga suka kai hari.
Odutola, ya ce ‘yan sanda sun kama wani Awada Ishaya daga jihar Filato a matsayin wanda ake zargi da aikata laifin.
An ce an dauki Ishaya aiki ne makonni biyu da suka gabata a matsayin mai gadi lokacin da aka bude wurin taron.
Karin labari: Gwamnatin jihar Kwara ta rufe kasuwar saida nama ta Mandate
“Rahoto daga sashin Iperu ya nuna cewa an yi garkuwa da mutane da kuma kisan kai a ranar 19 ga watan Afrilu, 2024, da misalin karfe 9:20 na dare.
“Shaidun gani da ido sun iya kirga wasu mutane takwas sanye da bakaken kaya dauke da bindigu sun fito daga wani wuri da ba a san ko su waye ba a cikin dakin shakatawa inda daga bisani aka harbe wani mutum daya malami a jami’ar Babcock mai suna Olowojobi Yinka a kirji.
“An kai malamin asibitin koyarwa na Jami’ar Babcock, inda aka tabbatar da mutuwarsa, haka kuma ana nan ana kokarin kamo masu laifin tare da kubutar da wadanda aka sace.”