Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kaduna, ta ce ta kama wani direban Kamfanin BUA da ya murkushe mutane shida har lahira tare da jikkata wasu 30 a hanyar Kano zuwa Zariya.
Kwamandan sashin, Mista Kabir Nadabo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, ranar Juma’a a Kaduna.
Nadabo ya ce musabbabin hadarin ya faru ne sakamakon wuce gona da iri da matukin mota ya yi.
Ya bayyana cewa hatsarin titin ya afku ne a ranar Alhamis, inda ya ce, “Wani direban tirela da ke jigilar buhunan shinkafa daga Kano zuwa Warri a Delta ya yi hatsari shi kadai a Wambai da ke kan hanyar Kano zuwa Zariya.”