Zulum ya yi Allah wadai da harin masallaci a Maiduguri, ya yi kira da a  ƙara yin taka tsantsan

IMG 20240429 WA0006 750x430

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin kunar bakin wake da aka kai wani masallaci a kasuwar Gamboru da ke birnin Maiduguri, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu talatin da biyar.

Harin ya faru ne da yammacin Laraba a lokacin sallar magriba, inda gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin imani da tauye alfarmar addini da rayuwar bil’adama.

Wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya fitar ta bayyana cewa ana zargin wani ɗan kunar bakin wake ya shiga masallacin a lokacin da masu ibada ke tsaka da gudanar da sallar Magariba.

Gwamna Babagana Zulum ya bayyana alhininsa kan abin da ya faru, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, sannan ya yi addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.

Ya kuma yi kira ga jama’a da hukumomin tsaro da su ƙara taka tsantsan, musamman a masallatai da sauran wuraren taruwar jama’a, duba da shagulgulan bukukuwa da ake ciki.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Borno tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro sun ɗauki matakai masu ƙarfi domin hana faruwar duk wata ɓarna ta tsaro a lokacin bukukuwa da bayan su.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here