Super Eagles: Ahmed Musa da wasu sun yi kira a daina sukar dan wasa Iwobi

Ahmed Musa, Super Eagles, Iwobi, AFCON
Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa da sauran ‘yan wasan kwallon kafa a tawagar kasar nan, sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina cin zarafin abokin...

Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa da sauran ‘yan wasan kwallon kafa a tawagar kasar nan, sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina cin zarafin abokin sana’arsu Alex Iwobi a yanar gizo bayan da Najeriya ta sha kashi a hannun kwaddebuwa da ci 2 da 1 a wasan karshe na AFCON.

A cewar wata majiya Iwobi wanda ke buga wasan tsakiya a kulob din Fulham na Premier da kuma kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ya goge dukkan hotunansa da bidiyonsa a shafinsa na Instagram bayan sukar da magoya bayan kwallon kafa suka yi masa.

Dan wasan ya taka leda na tsawon mintuna 79 yayin da Eagles ta kasa karawa gasar cin kofin AFCON guda uku bayan da Aibrikos ta doke Najeriya da lashe gasar.

Karanta wannan: “Najeriya Talaka Ce” – Martanin fadar Shugaban Kasa ga Sarkin Kano

Duk da haka Ahmed Musa ya yi amfani da shafinsa na X wajen yin kira ga zaman lafiya da juna yayin da ya bukaci magoya bayan kwallon kafa da su yabawa ‘yan wasan saboda rawar da suka taka a gasar ta AFCON.

“Ya ku masoya, Ina so in roƙe ku da ku dakatar da kushe abokin sana’ar mu Alex Iwobi ta yanar gizo, an yi iƙirarin cewa ƙwallon ƙafa ne ya haɗa mu yayin da muka shiga irin wannan hali.

“Rashin nasara babu shakka yana da wahala, amma niyya ga dan wasa guda don gazawar kungiyar rashin adalci ne domin mun yi nasara a kungiyance, kuma mun yi rashin nasara a kungiyance, Alex ya ba da gudunmawa a filin wasa kamar kowane memba na tawagarmu.

Karanta wannan: Yanzu-yanzu: Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun halarci taron Gwamnoni a Abuja

“Maimakon yada wasu maganganu ya kamata mu nuna ƙauna da goyon baya ga ‘yan wasanmu, suna bukatar ƙarfafawarmu fiye da kowane lokaci mu so junanmu sannan mu kaunaci juna” A sakon da Musa ya wallafa.

Haka kuma wasu ‘yan wasan kwallon kafa sun yada hotunan Iwobi a shafinsu na sada zumunta inda suke kare shi saboda kwazonsa a gasar AFCON da aka kammala a kwanan nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here