Yan sanda sun fara binciken lafiyar sabbin jami’an da za a dauka na shekarar 2022 a matsayin konsitabulari

police recruits new

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara aikin tantance lafiyar yan sandan da aka zaba a cikin shirin daukar sabbin jami’an ‘yan sanda na shekarar 2022.

An fara tantancewar a ranar 26 ga Fabrairun 2025, har zuwa ranar 12 ga Maris 2025, a hedikwatar Yan Sanda ta 17 da aka kebe a duk fadin kasar nan.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Alhamis, 27 ga watan Fabrairun 2025, ya ce tuni aka fara aikin tantance lafiyar su.

Ya tabbatar da cewa tun daga lokacin da aka fara aikin tantance lafiyar jami’an na shekarar 2022 ta hanyar amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa tun a ranar 5-6 ga Maris, 2024, yanzu hakan an gayyaci rukunin farko na ‘yan sandan sa suka samu nasara don horarwa.

Karanta: Kebbi: ‘Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane hudu, tare da ceto mutane

Rundunar ta bukaci sabbin jami’an da suka shiga cikin tsarin gwaji ta CBT su duba matsayin sakamakon su ta hanyar tashar daukar ma’aikata, apply.policerecruitment.gov.ng da takardar daukan aiki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here