Kebbi: ‘Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane hudu, tare da ceto mutane

Police badge

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta yi nasarar kashe wasu masu garkuwa da mutane hudu sannan ta kama daya, sannan ta kubutar da wani dattijo mai shekaru 60 mai suna Umaru Bawa a karamar hukumar Suru da ke jihar.

Haka kuma, ‘yan sandan sun kwato kudi Naira miliyan 3, wadanda tuni aka biya su a matsayin kudin fansa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar ya rabawa manema labarai a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 14 ga Fabrairu, 2025, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Gobiraje da ke karamar hukumar Suru tare da yin garkuwa da Bawa.

Karin labari: Sufeto Janar na Yan sanda ya rubutawa majalisar dattawa wasika kan ta rika binciken sirri kan bacewar bindigogi

“Bayan samun rahoton, jami’in ‘yan sanda na Suru (DPO) na Suru ya yi gaggawar tura jami’an ‘yan sanda da ’yan banga, inda suka bi diddigin wadanda ake zargin zuwa dajin Dakingari, inda aka yi artabu tsakanin jami’an tsaro da masu garkuwa da mutane, lamarin da ya kai ga kashe masu garkuwa da mutane hudu tare da kama mutum daya da ake zargi ya raunata”. in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, CP Bello M Sani, ya yabawa jami’an bisa jajircewa da kwarewa da suka nuna da kuma gaggawar mayar da martani.

Rundunar, duk da haka, ta bukaci mazauna yankin da su tuntubi jami’an tsaro ko kuma su kai rahoton duk wani motsi da ba su amince da shi ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here