Babban jami’in Binance ya dage cewa jami’an gwamnatin Najeriya sun bukaci cin hanci daga gare shi

Tigran Gambaryan

Babban jami’in Binance, Tigran Gambaryan ya dage cewa jami’an Najeriya sun bukaci cin hanci daga gare shi duk da kin amincewa da gwamnatin tarayya ta yi.

Gambaryan, wanda ke matsayin shugaban masu hada haɗar kudin internet, an tsare shi a Najeriya tun a watan Fabrairu zuwa Oktoban 2024.

A cewar gwamnatin tarayya, kama shi wani bangare ne na bincike mai zurfi kan zargin karkatar da kudade da kuma tabarbarewar tattalin arziki da ake dangantawa da ayyukan Binance a Najeriya.

Da yake ba da labarin abin da ya faru a cikin wani rubutu a shafin X, Gambaryan ya yi zargin cewa wasu ‘yan majalisar dokokin Najeriya sun nemi cin hanci mai yawa a cikin hada haɗar kudin internet na crypto, har ma ya zargi ‘yan majalisa uku da neman cin hancin dala miliyan 150.

Karanta:Majalisar wakilai ta amince da Naira Tiriliyan 54.99 a matsayin kasafin kudin 2025

Bugu da kari, ya yi ikirarin cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya nemi wasu makudan kudade daga hannun Binance saboda burinsa na siyasa.

A martanin da ya mayar, Mohammed Idris, ministan yada labarai na Najeriya, ya yi watsi da zargin Gambaryan da cewa “abin takaici ne da cin mutunci”.

Idris ya ce gwamnatin Najeriya ta ki amincewa da tayin dala miliyan 5 da Binance ta yi da nufin ganin an sako Gambaryan, inda ta zabi yin sulhu mai kyau da gwamnatin Amurka.

Ya ce ikirarin Gambaryan ba shi da gaskiya kuma da alama wani yunkuri ne na bata sunan jami’an Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here