Sabon shugaban kungiyar Hausa na kwalejin ilimi ta Aminu Kano hadin gwiwa da jami’ar tarayya ta Dutsen-ma ya sha rantsuwar kama aiki

IMG 20250215 WA0000

Sabon zababben shugaban kungiyar daliban Hausa na kwalejin ilmi ta Aminu Kano (AKCOE) hadin gwiwa da jami’ar tarayya da ke Dutsin-ma a jihar Katsina (FUDMA) kwamared Abubakar Sabo ya ce, zai hada kai da duk masu son ganin harshen Hausa ya cigaba da bunkasa, a ko ina suke don bunkasa harshen.

Kwamared sabo ya bayyana hakan ne jim kadan kadan bayan rantsar da shi da sauran shugabannin kungiyar a ranar Asabar.

A nasa jawabin shugaban kwalejin Dakta Ayuba Ahmad wanda ya sami wakilcin daraktan da ke kula da shirye-shiryen makarantar Dakta Dalladi Abdu, bukata ya yi ga sabbin shugabannin kungiyar da su zama jakadu na gari a duk in da suka sami kan su.

Karin karatu: BUK ta karawa Ministan Ilimi, Suleiman Yaradua, Muhammad Umar da wasu 63 matsayi zuwa farfesoshi

A jawaban su daban-daban daraktan da ke kula sashin dalibai a kwalejin wato Dean students affairs Dakta Ibrahim Muhammad da kuma shugaban sashin Hausa Dakta Mahe Isah Ahmad jan hankalin sabbin shugabannin suka yi da su kasanace masu hakuri da juriya da kuma riko da gaskiya da Amana.

Al’umma da dama ne suka sami halattar taron bikin kaddamarwar ciki har da sakataren kungiyar ‘yan jarida na jihar Kano kwamared Abubakar Shehu Kwaru, da shugaban kungiyar daliban makarantar kwamared Najib Kabir.

Cikin wadanda aka kaddamar akwai Rabi Ahmad Abubakar a matsayin mataimakiyar shugaba da Murja Murtala Muktar ma’aji da sauran su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here