Gwarzo ya taya murna ga sabon shugaban kungiyar tarayyar Afirka, ya bukace shi da ya hada kan kasashen

Mahmoud Ali Youssouf

Shugaban rukunin jami’o’in MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya taya ministan harkokin wajen Djibouti, Mahmoud Ali Youssouf, murnar zama shugaban kungiyar tarayyar Afirka (AU).

Gwarzo ya bukaci Youssouf da ya ba da fifiko kan hadin kai da ’yancin kai na Afirka, yana mai gargadin kada a daidaita da muradun kasashen yamma da ka iya kawo cikas ga ci gaban nahiyar.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa zaben da ya sa Youssouf ya samu nasara ya gudana ne a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia, inda Youssouf ya doke tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga inda ya lashe kujerar.

Karin labari: Ribadu, Elumelu, Saraki Suna Cikin ‘Yan Afrika 100 Da Sukai Fice – Rahoto

Odinga wanda ke samun goyon bayan shugaba William Ruto ya samu kuri’u 20 a zagayen farko, inda Mahmoud Ali Youssouf ya samu nasara a zagaye na bakwai da kuri’u 33.

Yayin da yake taya Mr. Yousouf wanda zai maye gurbin Moussa Paki, Gwarzo ya bayyana nasarar da ya samu a matsayin nasara ga Afirka, tare da yin kira gare shi da ya kara himma wajen ci gaban yankin Afrika.

Gwarzo wanda shi ne shugaban kungiyar kare hakkin ‘yan jarida a Afirka ya kuma yi kira ga Youssouf da ya yi amfani da ofishinsa wajen cimma duk wata manufa ta Afirka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here