Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu da Fasto Enoch Adeboye, babban mai kula da Cocin Redeemed Christian Church of God sun kasance cikin mutane 100 da suka fi fice a Afirka a shekarar 2025.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa jerin sunayen da aka fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta hanyar Reputation Poll International (RPI) tare da hadin gwiwar kungiyar Global Reputation Forum, na da sunayen wasu fitattun ‘yan Najeriya da shugabannin Afirka.
NAN ta kuma ruwaito cewa, jerin sunayen sun kunshi maza da mata daga sassa daban-daban na nahiyar da suka yi fice a fannin fasaha, masana’antu masu kere-kere, wasanni, hidimar jama’a, makarantun ilimi da kare muhalli.