Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, a ranar Litinin ya ce za a dawo da wutar lantarki a jihohi 17 na arewacin kasar da suka sha fama da matsalar wutar lantarki sakamakon lalacewar layin wutar lantarki na Shiroro-Kaduna.
Adelabu ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa manema labarai na Fadar Gwamnati jawabi bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a Abuja.
Ya ce katsewar wutar lantarkin zuwa yankin arewa na kasar ya faru ne sakamakon lalata layin wutar lantarki na Shiroro-Kaduna, wanda shine layin wuta mafi girma da ke kawo wuta zuwa arewa.
Ya kuma bayyana cewa za a gyara layin wutar cikin kwanaki uku zuwa biyar.
“Shugaban kasa ya umarci Mai Ba da Shawara Kan Tsaro, Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Shugaban Sojin Kasa da Shugaban Sojin Sama, su samar da tsaro ga mutanen da za su gyara layin wutar da aka lalata.
“Da an samu cikakken tsaro, ma’aikatan TCN za su sami kwarin gwiwa tare da masu gyaran layin su shiga fagen aiki su gyara layin.
“Don haka, ina rokon ‘yan’uwanmu da ke arewa su hakura, za mu dawo da wutar nan ba da dadewa ba, kuma ya kamata mu tsaya tare wajen kare babban layinmu na kasa don kauce wa sake lalacewa,” in ji ministan.
Ya kara da cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da kara wa Ma’aikatar Lantarki damar haɓaka layin wutar Shiroro-Kaduna, daya daga cikin tsofaffin layukan wutar kasar.
Ya ce idan aka kammala aikin haɓaka layin, arewa za ta samu wutar lantarki mai dorewa fiye da yadda ake samu yanzu.
Ya yi alkawarin ganawa da shugaban Hukumar Kula da Lantarki ta Najeriya (NERC) da dukkan Kamfanonin Rarraba Lantarki (DISCOs) don tabbatar da cewa ba a karbi kudi daga kwastomomi na arewa ba a lokacin da suka fuskanci matsalar wutar lantarki.
Adelabu ya bayyana cewa babban layin kasa ya rushe sau biyu kwanan nan sakamakon fashewar babbar na’ura a tashar Jeba.
Ya ce kafin fashewar, karon karshe da aka samu tangarda a layin wutar na kasa ya kasance kusan watanni hudu da suka gabata.
“Bari in fada muku gaskiyar lamarin: muna da tsofaffin kayayyakin aiki. Muna da layin wutar kasa da ya haura shekaru 50.
“Muna da layin wutar kasa mai rauni, hasumiyoyin suna durkushewa, kuma manyan wuraren sauya wuta da na’urorin suna tsofaffi.
“A gaskiya, babbar na’urar da ta fashe a Jeba tana da shekaru 47. Muna kokarin gyara wannan, mu sauya su, amma ba za a iya sauya duk su a lokaci daya ba,” in ji shi.
Ya ce ma’aikatar za ta ci gaba da sarrafa layin wutar don kauce wa matsaloli akai-akai har sai an kammala gyara shi dari bisa dari.