Manchester City dan wasan tsakiya, Rodri, ya lashe kyautar Ballon d’Or na bana, inda ya doke ‘yan wasan Real Madrid guda uku, Jude Bellingham, Vinicius Junior, da Dani Carvajal.
Dan wasan ƙasar Spain ya zama na biyu daga gasar Premier League da ya samu wannan gagarumar kyauta cikin shekaru 16 da suka gabata tun bayan Cristiano Ronaldo ya lashe ta a shekarar 2008.