Yar wasan Najeriya, Tobi Amusan ta kafa sabon tarihi bayan da ta lashe kyautar zinare a gudun mita 100 na gasar Commonwealth da aka yi a birnin Birmingham na kasar Birtaniya.
Mai shekaru 25, Yar wasan ta kafa sabon tarihin be, makwanni biyu bayan da ta zama ‘yar wasan Najeriya ta farko da ta lashe zinare a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya yayin da ta kai ga samun nasara a gasar tseren mita 100 na mata a Oregon.
Amusan, wacce ta shafe tarihin duniya a wasan kusa dana karshe na ban mamaki inda ta yi nasarar a filin Hayward a dakika ta 12.6.
Bayan da Amusan ta samu kyautar Zinare bayan lashe gasar.
Ita Kuwa ‘Yar kasar Jamaica Britany Anderson ta samu kyautar azurfa, yayin da zakarar Olympic Jasmine Camacho-Quinn ta Puerto Rico ta samu tagulla.
Amusan ta kafa tarihi a duniya a wasan dab da na kusa da na karshe, inda ta karya tarihin da Keni Harrison yar Amurka ta kafa a shekarar 2016.