Aminu Bala Madobi-daga Kano
Mafi Akasarin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a cikin wani jirgin kasa dake kan titin Abuja zuwa Kaduna a farkon wannan shekarar, har yanzu da yawa suna hannunsu, bayan da Yan ta’addan su suka yi watsi da yarjejeniyar da suka kulla da Gwamnatin Tarayya, kamar yadda jaridar PRNigeria ta rawaito.
Idan za a iya tunawa, Mummunan harin jirgin ya faru ne a ranar 28 ga watan Maris din wannan Shekarar ta 2022, lamarin da ya sanya da dama daga iyalan mutanen da aka yi garkuwa dasu cikin halin tsaka-me-wuya

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa akwai yarjejeniya tsakanin gwamnati da shugabannin kungiyar yan ta’adda da suka kai harin domin musanyen fasinjojin jirgin kasa da aka sace da wasu ‘yan ta’adda da aka kama kuma suke tsare a hannun jami’an tsaron Najeriya.
Wata majiya mai karfi a daya daga cikin hukumomin leken asirin da ke birnin Tarayya Abuja ta shaidawa jaridar PRNigeria cewa gwamnati ta dauki dukkan matakin da ya dace, amma yarjejeniyar ba ta hada da biyan kudin fansa ba don ganin an sako mutanen da aka sace din.
Majiyar wadda ta ki bayyana sunan ta ga jaridar PRNigeria, ta yi bayanin cewa gwamnati ta amince da yarjejeniyar musaye da ceto wadanda harin jirgin kasan ya rutsa da su domin kaucewa asarar rayuka.
A cewarsa, hukumar tsaro ta farin kaya DSS a wani shirin musayar yawu tace, ta saki ‘yan uwan su yan ta’adda kusan 30 da ake tsare da su galibi mata da kananan yara.
“Hakika, matar da ta haifi tagwaye yayin do su ke tsare an mika ta ga iyayenta,” in ji shi.
Rahotanni sun ce maimakon mutunta yarjejeniyar musanya da ‘yan ta’addan, in ji majiyar, sun sake yin garkuwa da fasinjoji goma sha daya bayan 63 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce: “Baya ga soke yarjejeniyar, sun kasance suna sakin wadanda abin ya shafa cikin rukunai ta hanyar da ba ta dace ba.
“Yanzu suna amfani da yanayi don karbar kudin fansa a wajen iyalan abin ya shafa.













































