Fursunoni 16 sun tsere daga gidan gyaran hali da ke Keffi

Kuje Prison1

Fursunoni 16 ne suka tsere daga gidan gyaran halin da ake tsare da su a birnin Keffi na jihar Nasarawa yau Talata.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiya bayan cin zarafin da ɗaurarrun suka yi wa jami’an tsaron gidan, kamar yadda mai magana da yawun hukumar gidan yari ta Najeriya Umar Abubakar ya rubuta a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce, Fursunonin sun yi galaba a kan ma’aikatan da ke bakin aiki a lokacin tashintaahinar.

“Wasu fursunoni sun keta tsaron gidan, inda suka kai hari kan jami’an da ke bakin aiki domin shawo kan lamarin, wanda hakan ya bai wa fursunonin 16 damar tserewa daga gidan yarin.

Sai dai ana ci gaba da ƙoƙarin ganowa tare da kamo ɗaurarrun da suka tsere.

Yayin wannan hargitsi jami’an gidan gyaran hali guda biyar sun samu manyan raunika.

Shugaban hukumar gidan gyaran hali na ƙasa Sylvester Nwakuche, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, kuma ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan guduwar.

Haka kuma Nwakuche ya yi gargadin cewa duk wani ma’aikacin da aka samu da hannu wajen tserewa za a hukunta shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here