BUK ta karawa Ministan Ilimi, Suleiman Yaradua, Muhammad Umar da wasu 63 matsayi zuwa farfesoshi

education minister Suwaiba Ahmed 750x430

 

Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta sanar da karin girma ga malamai 66 zuwa matakin farfesoshi da mataimakan farfesoshi a shekarar 2024.

A wata sanarwa da Lamara Garba, Mataimakin Rajistara kuma Shugaban Sashen Harkokin Jama’a ya fitar, an bayyana cewa an daga darajar malamai 44 zuwa farfesoshi, yayin da 22 suka zama mataimakan farfesoshi.

Sanarwar ta ce karin girman na nuna jajircewar jami’ar wajen yaba wa kwazon malamai.

Daga cikin wadanda aka daukaka darajar akwai Ministar Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, Suleiman Mainasara Yaradua, da Muhammad Sani Umar Musa.

An kuma tabbatar wa ma’aikata cewa za a ci gaba da bin ka’idojin daukaka don adalci da gaskiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here