Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana adawa da kudirin gyaran haraji da ke gaban Majalisar Tarayya, tana mai cewa zai kara wahalar da rayuwar al’umma.
Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana matsayar gwamnatin a lokacin bikin Sabuwar Shekara a Filin Mahaha, Kofar Naisa.
A wata sanarwa daga Ibrahim Garba Shu’aibu, Babban Sakataren Yada Labarai na mataimakin gwamnan, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kudirin harajin a matsayin wanda bai dace ba kuma zai kara wa ‘yan kasa wahala.
Ya ce maimakon haka, ya kamata a mayar da hankali kan yaki da talauci da yunwa, musamman a Arewa.
Gwamnan ya kuma jaddada nasarorin gwamnatinsa a bangaren lafiya, ilimi, gine-ginen hanyoyi, da tallafin karatu a kasashen waje.
Haka zalika, ya yabawa dawo da Muhammadu Sanusi II matsayin Sarki a 2024, yana mai cewa al’ummar Kano su zauna lafiya da juna.
Ya bukaci jama’a su hada kai don ciyar da Kano gaba a 2025.