Jam’iyyar NNPP ta ayyana Sanata Rufa’i Sani Hanga a matsayin dan takararta na Sanatan Kano ta tsakiya bayan ficewar tsohon Gwamna Malam Shekarau daga jam’iyyar.
Wannan ya biyo bayan zaben fidda gwanin da jam’iyyar ta gudanar da maraicen ranar Alhamis, a cibiyar matasa ta Sani Abacha.
Bayan kammala zaben Shugaban Jam’iyyar NNPP na Kano ta Tsakiya, Abdullahi Zubair, shi ya jagoranci taron tabbatar da Dan takarar domin cike gibin da tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau ya bari.
Malam Shekarau ya bar jam’iyyar NNPP zuwa PDP, bayan wasu rigingimun da ba a kai ga warware wa ba dangane da batun rabon takara a jam’iyyar.
Sai dai babu tabbas ko INEC za ta amince da maye gurbin Shekarau din da Hanga saboda wa’adin maye gurbin dan takara da hukumar zabe ta kayyade ya wuce.











































