A ranar Alhamis ne majalisar wakilai ta zartas da kudurin dokar gyaran dokar zabe bayan ta yi kwaskwarima kan batun tilastawa yin zaben fidda gwani na kai tsaye.
An karanto kudirin dokar a karo na uku kuma an zartar da shi yayin zaman majalisar a yau.
Majalisar a zamanta na ranar Laraba ta cire wani sashi na 84 da ke bukatar jam’iyyun siyasa su zabi ‘yan takara ta hanyar zaben fidda gwani kai tsaye.
Sadarar da aka yi wa kwaskwarima ta ce: “Tsarin tantance ‘yan takara da jam’iyyun siyasa za su yi a mukamai daban-daban za su kasance ta hanyar fidda gwani kai tsaye ko kuma wanda bana kai tsaye ba.”
Majalisun dokokin kasar za su mayar da kudirin ga shugaban kasa bayan da majalisar wakilai ta amince da shi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudurin dokar, saboda rashin amincewarsa da matakin farko na zaben fidda gwani na kai tsaye.
Majalisar dattijai da majalisar wakilai sun amince da kudirin a watan Yulin 2021 kuma sun amince da zaben fidda gwani na dukkan jam’iyyun siyasa.












































