‘Yan sanda sun farwa masu garkuwa da mutane tare da kama wasu a Abuja

masu, garkuwa, mutane, abuja, farwa, 'yan sanda, kama
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayyar Abuja, a wani sumame tare da wasu jami’an tsaro, sun kai samame sansanonin masu garkuwa da mutane a kan iyakokin...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayyar Abuja, a wani sumame tare da wasu jami’an tsaro, sun kai samame sansanonin masu garkuwa da mutane a kan iyakokin Abuja ranar Juma’a.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin X a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Jami’an rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, tare da hadin gwiwar runduna ta musamman ta Guards Brigade da na DSS, a ci gaba da kokarin yaki da miyagun ayyuka a FCT, a ranar 7 ga watan Yuni, 2024, da misalin karfe 10:00 na safe, inda suka yi aiki” in ji sanarwar.

Karin labari: Shugaba Tinubu ya sake sabbin nade-nade

Rahotanni sun bayyana cewa an kama wasu mutane hudu da ake zargina aikata garkuwa da mutane yankin.

Sanarwar ta kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa su ‘yan kungiyar ‘yan ta’adda ne mai suna “Mai One Million.”

Kungiyar ta “Mai One Million” ta ce tana da alhakin yin garkuwa da mutane da wasu munanan laifuka a babban birnin tarayyar Abuja da kewaye.

Karin labari: Hukumar EFCC ta kama wasu mutane 5 da ake zargi da yin damfara a Abuja

An bayyana cewa an yi artabu tsakanin ‘yan bindigar da jami’an tsaro, lamarin da ya tilastawa ‘yan bindigar tserewa.

Jami’an tsaron sun kuma ceto wadanda lamarin ya rutsa da su da aka ce an sake haduwa da iyalansu, kuma gidajen da masu garkuwa da mutane suka gina ba bisa ka’ida ba a duk sansanonin da ake sintiri duk sun lalace.

A cikin sanarwar, kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayyar Abuja, CP Benneth Igweh, ya yaba da nasarar da aka samu tare da yin kira ga mazauna yankin da su kasance cikin taka-tsantsan tare da bayar da rahoton abubuwan da ake zargi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here