Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Nkiruka Maduekwe a matsayin babban darakta kuma babban jami’in zartarwa na Majalisar Kasa kan Sauyin Yanayi, wanda ke jiran kwamitin sa ido na NCCC ya tabbatar da hakan.
Mai taimakawa shugaban kasa Ajuri Ngelale ne ya sanar da nadin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ya ce nadin ya biyo bayan kudirin shugaban kasar na ganin an tabbatar da aniyar Najeriya kan masana’antu.
Karin labari: Hukumar EFCC ta kama wasu mutane 5 da ake zargi da yin damfara a Abuja
Mista Ngelale ya ce hakan ya karawa masu saka hannun jari kwarin gwiwa tare da bude kimar tattalin arziki mai dorewa ta hanyar amfani da kudin yanayi daban-daban.
Ya ce shugaban ya kuma amince da cewa Misis Maduekwe, mai shekaru 39, za ta yi aiki a matsayin shugabar kwamitin kula da harkokin kasuwancin Carbon ta kasa (NCMAP).
Mista Ngelale ya ce shugaban kasar ya kuma amince da nadin Ibrahim Abdullahi Shelleng mai shekaru 40 a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin kudi da hulda da masu ruwa da tsaki a ofishin shugaban kasa.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Ministan kudi ya gabatar da sabon tsarin mafi karancin albashi
Mista Shelleng dai yana goyon bayan sakatariyar majalisar kula da sauyin yanayi ta kasa (NCCC), inda zai gudanar da dukkan al’amuran da suka shafi harkokin kudi da kuma huldar masu ruwa da tsaki da masu ba da tallafi.
Mista Ngelale ya ce shugaban kasar ya amince da Mista Shelleng a matsayin Sakataren Kwamitin Tsare-tsare na Kasuwar Carbon ta Kasa (NCMAP).
Ya kara da cewa shugaban kasar ya kuma amince da nadin Olamide Fagbuji mai shekaru 44 a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan fasahar yanayi da ayyuka na ofishin shugaban kasa.
Karin labari: Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da shirin bai wa ƙananan ƴan kasuwa bashi
“Bisa umarnin shugaban kasa, nade-naden da aka ambata sun fara aiki nan take, in ji sanarwar.”
Sanarwar ta kara da cewa, “Shugaban na sa ran sabbin wadanda aka nada za su kawo kwarewarsu da kuma da’a da za su iya aiwatar da wadannan muhimman ayyuka don tabbatar da burin kasar nan na ci gaban masana’antu kore da kuma ayyukan sauyin yanayi don samun ci gaba mai dorewa da ci gaban kasa” kamar yadda NAN ta tabbatar.