Da Dumi-Dumi: Ministan kudi ya gabatar da sabon tsarin mafi karancin albashi

Wale, Edun, Tinubu, Ministan, kudi, gabatar, sabon, tsarin, mafi, karancin, albashi, najeriya
Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya gabatar da sabon tsarin mafi karancin albashi ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya cika...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya gabatar da sabon tsarin mafi karancin albashi ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya cika sa’o’i 48.

Edun, tare da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Atiku Bagudu, sun gabatar wa Shugaba Tinubu abubuwan da suka shafi sabon mafi karancin albashi a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa a Abuja, ranar Alhamis.

Karin labari: Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da shirin bai wa ƙananan ƴan kasuwa bashi

A cewar Western Post, sabon kudirin ya nuna cewa za a rika biyan mafi karancin albashi na Naira Dubu 105,000 (kimanin dala $220) a kowane wata ga ma’aikatan Najeriya.

A halin yanzu Tinubu yana nazarin wannan shawara, kuma ana sa ran sanarwar hukuma nan ba da dadewa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here