Iran ta kama jirgin dakon man Amurka a matsayin ramuwar gayya

1682630945218
1682630945218

Rundunar sojin ruwan Amurka ta ce Iran ta kama wani jirgin ruwanta mai dakon mai a mashigin tekun Oman.

Hakan na zuwa ne bayan ta buƙaci sakin jirgin mai ɗauke da tutar tsibirin Marshal cikin gaggawa, tare da ayyana matakin da Iran din ta ɗauka a matsayin abin da ya saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa.

Amurka ta ce dakarun juyin juya hali na Iran ne suka yi kamen, Iran ta ce kama jiragen ruwa martani ne kan matakan da aka ɗauka a kan ta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here