Rikicin Sudan: Daliban Najeriya sun isa kasar Masar – Gwamnatin tarayya

C82C71CE 6A02 4B86 B8A3 15F4188079D8
C82C71CE 6A02 4B86 B8A3 15F4188079D8

Rukunin farko na daliban Najeriya da aka kwashe daga kasar Sudan sun isa kan iyakar Aswan a kasar Masar a ranar Alhamis 27 ga watan Afrilu.

shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM) Abike Dabiri-Erewa ta bayyana hakan ta shafinta na Twitter a daren Alhamis.

”rukuni na farko ya isa kan iyakar Aswan a Masar, amma an riga an rufe iyakar. Za su tashi da sassafe sannan su wuce filin jirgin sama,” a cewar bayanin

Hakazalika, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa ta ce rukunin farko na ‘yan Najeriya daga Sudan sun riga sun isa iyakar Masar kuma za a kai su Najeriya a yau Juma’a.

Mataimaki na musamman ga Darakta Janar na NEMA, Idris Muhammad, ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Channels, inda ya tabbatar da isowar rukunin farko na ‘yan Najeriya a kan iyakar Masar.

Saidai Muhammad ya musanta labarin ‘yan Najeriya da suka tsere daga Sudan da suka makale a cikin hamada saboda rashin biyan masu jigilar kaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here