Mutum na farko ya mutu a Birtaniyya sakamakon sabuwar kwayar cutar Covid-19 mai suna Omicron.
Firaministan Birtaniyya Boris Johnson ya tabbatar da hakan lokacin da ya kai ziyara cibiyar da ake yin allurar rigakafin cutar a Paddington kusa da yammacin London.
Ya nuna rashin jin dadin kan yadda cutar ke sanadiyyar kwantar da mutane a asibiti, inda ya ce za su duba ko akwai yiwuwar kara kafa wasu dokoki domin kare yaduwar cutar a kasar ta Birtaniyya.
Sakataren lafiya na kasar Sajid Javid ya ce gwamatin kasar ta kudiri aniyar yi wa mutane miliyan daya allura rigakafin cutar a ko wace rana daga yanzu har zuwa karshen shekarar nan.













































