Gwamnatin jihar Katsina ta gayyaci Malam Yahaya Masusauka domin ya bayyana matsayin sa kan zargin cewa koyarwarsa tana saɓa ƙa’idojin addinin musulunci a lokacin wa’azinsa.
Wannan na cikin sanarwar da sakataren gwamnatin jiha Abdullahi Faskari ya fitar ta hannun daraktan yaɗa labarai Ibrahim Almu Gafai a cikin birnin Katsina ranar talata.
Sanarwar ta nuna cewa gwamnati ta karɓi koke daga jama’a na cewa kalaman da masusauka yake yi a yayin wa’azi ba su yi daidai da ka’idojin addini ba.
Haka kuma an sami ƙarin korafi daga ɓangaren masusauka cewa wasu mambobin ƙungiyar jama’atu izalatul bidia suna zaginsa tare da barazanar kai masa hari.
Gwamnati ta tura batun zuwa majalisar masarautar katsina domin a saurari bangarorin biyu, inda aka kira su domin gabatar da bayanansu.
Sarkin katsina abdulmuminu kabir usman ya jaddada cewa ba a yarda wani ya yi wa’azi ko koyarwa ta hanyar da za ta cutar da wani ko ta haddasa rikici ba.
Domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito, gwamna Dikko Radda ya umurci masusauka da ya shirya don ya kare kansa a gaban kwamitin malamai na musamman da aka kafa don sauraron zarge zargen da ake masa.
Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin jiha ta ɗauka domin warware matsalar kamar yadda ya kamata.
Sanarwar ta kara bayyana cewa daga yanzu gwamnati za ta kafa ƙa’idoji ga masu wa’azi da malamai a fadin jihar, tare da gargadin cewa duk wanda ya karya su za a dauki matakin da ya dace a kansa.
Faskari ya roki jama’ar jihar da su kwantar da hankalinsu saboda gwamnati na gudanar da lamarin cikin adalci da bin ka’ida.
NAN













































