Muhuyi Magaji ya tabbatar da karbar miliyan biyar da dubu dari bakwai wanda kotu ta tilastawa Ganduje ya biyashi

Muhuyi Magaji KANO
Muhuyi Magaji KANO

Dakatattacen shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin-hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya tabbatar da karbar naira miliyan biyar da dubu dari bakwai na albashinsa na tsawon lokacin da aka dakatar da shi ba bisa ka’idaba, kamar yadda kotu ta bayar da umarni a baya.

Rimingado ya tabbatar da karbar kudin ne a ranar Alhamis da safe, inda yace zai yi amfani da kudin wajan tallafawa marasa karfi.

A ranar Talata kotun ma’aikata dake Abuja ta bawa bankin GTBank uamarni da ya biya Rimingado duk hakkokin sa daga lokacin da gwamantin kano ta dakatar da shi ba bisa lka’ida ba a shekarar 2021.

Idon zaku iya tunawa a baya dai gwamnan Kano ya dakatar da Rimingado sakamakon binciko wata badakala ta kwangila da ake zargi tana da alaka da iyalan gwamna Ganduje.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here