Harin Borno: Tinubu ya umurci sojoji su sake duba tsare-tsaren yaƙi da Ta’addanci

President Bola Tinubu 1 1 750x430

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar da umarnin Shugaba Bola Tinubu ga rundunar sojin Najeriya da su sake nazari kan dabarun yaki da ƙungiyoyin ta’addanci a faɗin ƙasar.

Wannan ya haɗa da tura manyan kayan aikin soja na zamani da na’urorin leƙen asiri domin kawar da ‘yan ta’adda.

Shettima ya bayyana hakan ne a sakon ta’aziyya da ya aika wa Gwamna Babagana Umara Zulum da al’ummar Borno, bisa harin ta’addanci da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama a kauyen Darajamal na Ƙaramar Hukumar Bama. Ya ce wannan babban rashi ne ga jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, duk da wannan alhini, gwamnati da dakarun Najeriya za su tabbatar da ganin an tabbatar wa iyalan waɗanda suka rasu da adalci.

Karin karatu: Yan Bindiga sun sace mai daƙin shugaban jam’iyyar APC da Ƴarsa a jihar Kwara

Ya kuma nuna kwarin gwiwa kan ƙarfin rundunar sojin Najeriya wajen shawo kan kalubalen tsaro da ake fuskanta.

Shettima ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya amince da ƙarin sayen jiragen leƙen asiri (drones), tare da bayar da umarnin cewa dukkan hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen sake nazarin dabarun ayyukansu.

Haka kuma, ya ce gwamnati na duba yiwuwar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, domin magance matsalolin tsaro da ke buƙatar ƙananan sassa na musamman waɗanda suka fahimci yanayin yankin da al’adu, tare da iya aiki kafada da kafada da al’umma a matakin ƙasa.

Ya roƙi Allah ya jikanta waɗanda suka rasa rayukansu tare da ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafawa jihar da iyalan da abin ya shafa wajen magance wannan matsala ta tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here