Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin hana jam’iyyar PDP na kasa rusa shugabacin jam’iyyar Kano.
Mai shari’a Taiwo O. Taiwo, a ranar Talatar da ya gargadi jam’iyyar PDP cewa ta bar shugabancin jam’iyyar PDP na Kano daga mazabu zuwa jiha su ci gaba da gudanar da aiki har sai an yanke hukunci.
Solacebase ta ruwaito cewa wadanda suka shigar da karar su ne Shehu Wada Sagagi da Bashir Tanko Muhammaed da Ali Tijani Ansaru da Gambo Jamil Abba yayin da wadanda ake karan su ne jam’iyyar PDP da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Idan dai za a iya tunawa a makon da ya gabata wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP sun yi wani taron manema labarai a Kano inda suka bukaci a rusa shugabannin jam’iyyar a Kano.
A cewar masu ruwa da tsakin shugabannin jam’iyyar a jihar, magoya bayan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne wanda ya koma NNPP tare da zargin yunkurin dagula al’amuran jam’iyyar PDP a jihar.












































