A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu a jihar.
SolaceBase ta ruwaitu cewa majalisar ta yi karatun farko na kudirin kafin su fara hutun da suka koma jiya.
Bayan karatu na biyu da na uku na kudurin, mataimakin kakakin majalisar, Muhammad Bello Butubutu, ya yunkuro domin amincewa da kudurin.
Kakakin majalisar Jibril Ismail Falgore ne ya jagoranci zaman majalisar.
Sabbin masarautun masu daraja ta biyu da za a kirkiro sun hada da:
1. Masarautar Rano: Rano- Bunkure, Kibiya
2. Masarautar Karaye: Karaye- Rogo
3. Masarautar Gaya: Gaya- Ajingi, Albasu