Jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, ya soki majalisar dokokin jihar Kano da zartar da kudurin dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu a ranar Talata a jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin cin karo da umarnin kotu.
Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa majalisar dokokin jihar Kano a ranar Talata ta zartar da kudirin kafa masarautu guda uku tare da masu daraja ta biyu.
Masarautun sun hada da Masarautar Gaya da Rano da kuma Karaye.
Kwankwaso ya bayyana cewa tuni babbar kotun tarayya da ke Kano ta umarci dukkan bangarorin da ke da ruwa da tsaki a rikicin masarautar Kano da su ci gaba da kasancewa a halin yanzu.
Karin labari: Yanzu-yanzu: Wani Dan Majalisar Wakilan Najeriya ya rasu
Ya yi wadannan kalamai ne ranar Talata a Kano a wata hira da SolaceBase.
Ya kuma jaddada cewa, bisa ka’ida, Kano har yanzu tana da sarakuna biyar masu daraja ta daya, kuma babu wani tanadi da aka yi wa sarakunan masu daraja ta biyu a jihar.
“Duk da cewa ni ba lauya ba ne, amma dokokinmu sun nuna karara cewa shari’ar tana gaban kotu, kuma har yanzu muna da sarakuna biyar masu daraja ta daya,” in ji shi. “Abin da Majalisar ta yi, a ganina, bata lokaci ne. Dole ne su jira hukuncin kotu kan wannan batu.”
Ya kara da cewa ko da majalisar dokokin jihar Kano za ta samar da sarakuna masu daraja ta biyu, mutanen Rano, Karaye, Gaya, da Bichi ba za su taba jin dadin wannan doka ba.
Karin labari: DA DUMI-DUMI: Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu
Tsohon Kwamishinan Raya Karkara ya kuma zargi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tada zaune tsaye a Jihar Kano da kokarin yi mata zagon kasa.
Da yake tsokaci kan kudirin da Kawu Sumaila ya gabatar a zauren majalisar wakilai na kafa jihar Tiga a Kano, Musa Kwankwaso ya bayyana goyon bayansa, yana mai kallon hakan a matsayin wata dama ce ga jam’iyyar APC ta mulki Kano.
“Wannan kudiri da Kawu Sumaila ya gabatar abu ne mai kyau, kuma na yi farin ciki da hakan. Da zarar kudirin ya tsallake karatu na uku a majalisar dokokin kasar, za a sake yin wani zabe a Kano, kuma ko shakka babu jam’iyyar APC za ta yi nasara saboda mutanen Kano sun fusata da gwamnatin NNPP” in ji Musa.