Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan kudirin kafa masarautu 3

Abba, Kabir, Yusuf, rattaba, hannu, kudirin, kafa, masarautu
A ranar Talata ne Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan dokar kafa majalisar masarautu ta jihar Kano na shekarar 2024, matakin da ake sa...

A ranar Talata ne Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan dokar kafa majalisar masarautu ta jihar Kano na shekarar 2024, matakin da ake sa ran zai kare al’adun gargajiyar jihar.

NAN ta rawaito cewa majalisar dokokin jihar ta zartar da dokar.

Ya bayyana cewa Masarautar Rano ta kunshi kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure.

Karin labari: “Kirkirar Masarautu 3 a Kano ya saba umarnin Kotu” – Jigon APC

Da yake jawabi bayan sanya hannu kan kudirin dokar,  Abba Kabir Yusuf, ya jaddada mahimmancin sabuwar dokar wajen dorewar kyawawan dabi’u da dabi’un al’ummar jihar.

Ya ce dokar za ta dinke barakar da ke tsakanin talakawa da gwamnati.

Kamar yadda doka ta tanada, Majalisar Masarautar Kano da ake da ita, karkashin jagorancin Sarki mai daraja ta daya a matsayin shugaba, za ta samu goyon bayan masarautun masu daraja ta biyu a Rano, Gaya, da kuma Karaye.

Karin labari: DA DUMI-DUMI: Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu

Gwamnan ya kara da cewa daga baya za a bayyana sunayen sabbin sarakunan masu daraja ta biyu.

Mahukuntan masarautu masu daraja ta biyu zai takaita ne a kananan hukumominsu.

Kakakin majalisar, Jibrin Falgore, ya nanata kudurin majalisar na zartar da dokokin da ke inganta rayuwar al’ummar jihar.

Ana sa ran wannan ci gaban zai yi tasiri mai kyau ga tsarin mulkin jihar kamar yadda NAN ta tabbatar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here