Hajjin Bana: Hukumar NDLEA ta kama alhazai da ke ta’ammali da kwayoyi

NDLEA, Hajjin, Bana, Hukumar, NDLEA, kama, alhazai, ta'ammali, kwayoyi
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun kai samame otal din Emerald da ke unguwar Ladipo a Oshodi, jihar Legas, inda aka kai wasu...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun kai samame otal din Emerald da ke unguwar Ladipo a Oshodi, jihar Legas, inda aka kai wasu maniyyata aikin hajjin bana a kasar Saudiyya, yayin da aka cafke su suna shan hodar iblis a gaban jirginsu na zuwa kasa mai tsarki ranar Laraba.

SolaceBase ta rawaito cewa wadanda aka kama a yayin samamen da hukumar leken asirin ta gudanar sun hada da Usman Kamorudeen mai shekaru 31 da Olasunkanmi Owolabi mai shekaru 46 sai kuma Fatai Yekini mai shekaru 38 da kuma wata mata Ayinla Kemi mai shekaru 34.

Karin labari: Tinubu zai kashe Tiriliyan biyar kan tallafin man fetur

A cewar wata sanarwa da Femi Babafemi, Daraktan NDLEA, a Abuja, ya fitar a ranar Alhamis, an ajiye mutanen hudu ne a dakuna biyu a cikin otal din inda suka shirya kwalaye 200 na hodar iblis da nauyinsu ya kai kilogiram 2.20 domin su sha ko su hadiye, yayin da jami’an hukumar ta NDLEA suka chafke su a dakunan da suke.

Da yake yabawa kwamandan da jami’an hukumar NDLEA reshen jihar Legas da suka gudanar da aikin, shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya ce hukumar za ta ci gaba da yada labaran ta domin gano bakin zaren.

Karin labari: Gwamnatin Kano za ta sake inganta wuraren shakatawa da lambuna

Tare da kama miyagu masu aikata laifuka waɗanda za su so su fake a ƙarƙashin aikin hajji don aiwatar da munanan ayyukansu da ke iya zubar da mutuncin ƙasar.

Shugaban NDLEA ya kuma bayyana cewa “Hukumar za ta yi aiki tare da takwarorinmu na Saudi Arabiya don tabbatar da cewa an gano wadanda aka kebe na haramtattun kayan da aka kama a kowane yanki na Saudi Arabiya kuma an magance su yadda ya kamata.

NDLEA

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here