Hajiya Hauwa’u Adamu, mahaifiyar fitaccen mawakin Hausa, Dauda Adamu, wanda aka fi sani da Rarara, ta shaki iskar‘yanci bayan shafe kwanaki 20 a hannunta masu garkuwa da mutane.
Rarara ne ya tabbatar da labarin sakin nata, a shafin sa na Instagram da aka tabbatar a safiyar Laraba.
Yayin da bayanai kan sakin mahaifiyar mai shekaru 75 ke ci gaba da yawo a kafafen sada zumunta, wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce an biya kudin fansa na wasu masu makudan miliyoyi kafin wadan da sukai garkuwar da ita su sake ta.
SolaceBase ta ruwaito cewa an sace Hajiya a jihar Katsina a watan da ya gabata.
A halin da ake ciki kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a baya ta sanar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da ita.