Hukumar zabe a Kaduna ta sanya ranar zaben Kananan Hukumomi

INEC, Hukumar, zabe, Kaduna, sanya, ranar, zaben, Kananan, Hukumomi
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta tsara gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar a ranar 19 ga watan Oktoba, 2024. Shugabar...

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta tsara gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar a ranar 19 ga watan Oktoba, 2024.

Shugabar hukumar, Hajara Mohammed, ta sanar da ranar a wani taron ranar Talata da jam’iyyun siyasa da sauran wadanda abin ya shafa a Kaduna.

Hajara, ta ce an rantsar da kansiloli a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2021 kuma za su kawo karshen wa’adinsu na shekaru uku a ranar 31 ga watan Oktoba, 2024.

“KAD-SIECOM ita ce ke da alhakin shirya zaben shugabanni da mataimakan shugabanni, da kansiloli a jihar.

Karin labari: Mahaifiyar Shahararriyar Mawakin Hausa da aka sace, Rarara ta shaki iskar ‘yanci

“A bisa tanadin sashe na 25 (1) na dokar KAD-SIECOM ta 2024, ana sanar da jama’a cewa za a gudanar da zaben kansilolin karamar hukumar Kaduna a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba, 2024, tsakanin karfe 8 na safe zuwa 4 na yamma.

“Hukumar ta fitar da jadawalin zaben a ranar Talata 16 ga watan Yuli 2024.” .

Shugabar ta ci gaba da cewa an fitar da ka’idojin zaben 2024 tare da jadawalin zaben.

Hajara Mohammed, ta tabbatarwa da bangarorin da abin ya shafa cewa hukumar a shirye take ta gudanar da zaben a ranar da aka sanya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here